Jonathan ya rantsar da majalisar ministocinsa. | Labarai | DW | 06.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jonathan ya rantsar da majalisar ministocinsa.

Muƙaddashin shugaban Nijeriya ya rantsar, tare da tura ministoci zuwa ma'aikatu

default

Muƙaddashin shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

Dazunnan ne muƙaddashin shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Jonathan ya rantsar da mambobin sabuwar majalisar ministocin sa, tare da tura su ma'aikatun da zasu kula da su. A yanzu dai Mr Oden Ajumogobia shi ne zai kula da ma'aikatar harkokin waje, a yayin da Deizani - Allison Maduekwe kuwa ta je ma'aikatar kula da harkokin man fetur a matsayin minista. Sai kuma Olusegun Aganga, wanda kamar yadda jaridu suka yi hasashe tunda farko, shine ya kasance ministan kula da harkokin kuɗi a Nijeriya. Sauran sune, Adetokunbo Kayode, wanda shi ne ministan kula da harkokin tsaro a Nijeriya, kana Murtala 'Yar'adua zai kasance ministan ƙasa a ma'aikatar kula da harkokin tsaron. Senata Bala Muhammad, shi ne a yanzu zai kula da Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya - a matsayin minista. Dakta Shamsuddeen Uthman, shi ne zai ci gaba riƙe muƙamin ministan kula da harkokin tsare-tsare, a yayin da itama Farfesa Dora Akunyili zata ci gaba da zama ministar kula da harkokin sadarwa.

A ranar Larabar data gabata ne dai, majalisar dattijan Nijeriya ta amince da mutane 38 ga muƙaman ministocin, bayan da tunda farko muƙaddashin shugaban ƙasar ya rusa tsohuwar majalisar ministocin - mai wakilai 42 kimanin makonni biyu gabannin hakan, kana kusan fiye da wata guda bayan da ya zama muƙaddashin shugaban ƙasa. Mambobin tsohuwar majalisar ministoci 14 ne suka dawo cikin sabuwar majalisar. Dakta Goodluck Jonathan ya zama muƙaddashin shugaban Nijeriya ne sakamakon rashin lafiyar da shugaban ƙasar, Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua ke fama da ita.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Abdullahi Tanko Bala