Johannes Rau ya rasu | Siyasa | DW | 27.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Johannes Rau ya rasu

A yau da sanyin safiya tsofon shugaban kasar Jamus Johannes Rau ya riga mu gidan gaskiya

Johannes Rau

Johannes Rau

A ranar sha shida ga watan janairu na 1931 ne aka haifi Johannes Rau wanda ya kasance daya daga cikin gaggan jami’an siyasar Jamus a cikin tarihinta na bayan yakin duniya na biyu. Kuma nadin shugaban kasa da aka yi a cikin watan mayun shekara ta 1999 ya kasance kololuwar sana’arsa ta siyasa. Marigayi Johannes Rau ya kutsa kai a harkar siyasa ne a cikin shekarun 1950 lokacin da ya shiga inuwar wata jam’iyyar siyasa mai taken All German People’s Party ko kuma GVP a takaice. Dalilinsa a game da shiga inuwar jam’iyyar, wacce a wancan lokaci take karkashin shugabancin Gustav Heineman tsofon shugaban kasar Jamus, shi ne saboda adawar da take yi na yi wa yammacin Jamus damarar makamai. Bayan wargajewar jam’iyyar a shekara ta 1957 Johannes Rau ya koma karkashin tutar jam’iyyar Social Democrats, wato SPD, inda a cikin dan gajeren lokaci ya samu ci gaba matuka ainun a sana’arsa ta siyasa. Domin kuwa shekara daya bayan komawarsa inuwar jam’iyyar ne ya samu wakilci a majalisar jihar Northrhine-Westfaliya. A shekarar 1967 ya zama daya daga cikin gaggan masu magana da yawun jam’iyyar a majalisa sannan shekaru uku bayan haka ya zama wakili a majalisar ministocin gwamnatin jihar ta Northrhine-Westfaliya. Yayi tasiri sosai da sosai a harkar ilimi a matsayinsa na ministan ilimi da binciken kimiyya da fasaha a jihar. A matsayinsa na shugaban reshen jam’iyyar SPD a matsayi na jiha an nada marigayi Johannes Rau gwamnan jihar Northrhine-Westfaliya a shekara ta 1976. Bayan shekaru 20 cir da yayi a matsayinsa na gwamna Johannes Rau yayi murabus a shekara ta 1998 ko da yake hakan ba ya ma’anar kawo karshen sana’arsa ta siyasa domin kuwa shekara daya bayan haka a 1999 an nada shi shugaban kasar Jamus a zagaye na biyu na kuri’ar raba gardama da majalisar tarayya ta kada. A cikin jawabin da ya gabatar dangane da nadinsa da aka yi Johannes Rau cewa yayi:

A matsayina na uban kasa ba zan yi sako-sako da alhakin da ya rataya a wuyana ba. Zan yi bakin kokarina wajen zama shugaban kasa ga illahirin Jamusawa kuma kofata a bude take ga kowa-da-kowa Ya-Allah Jamusawa ne ko bakin dake zaune a nan kasar suke kuma gudanar da ayyukansu a cikinta.

Da wannan bayanin marigayi Johannes Rau ya bayyana matsayinsa na shugaban kasa mai neman kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka a tsakanin dukkan jinsunan mutanen da Jamus ta kunsa.