1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jma´iyar SLPP a Sierra Leone ta shigar da ƙara a game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa

September 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuBI

Jam´iyar da ke riƙe da ragamar mulmi a ƙasar Sierra Leone, wato SLPP ta shigar da ƙara kotu, tare da buƙatar a dakatar da bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2.

Bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta bada sakamakon kashi 3 cikin 4, na runfunan zaɓe, ɗan takara jam´iyar adawa Ernest Koroma ke sahun gaba, tare da kashi kussan 60 cikin ɗari na ƙuri´un da aka jefa.

Kakakin jam´iyar SLPP, Victor Reider, ya ce sun shigar da wannan ƙara, ta la´akari da ɗimbin kura-kuren da ke tattare, da sakamakon da ake bayyanawar.

A jiya, jami´an tsaro sun tarwatsa zanga-zangar da magoya bayan jam´iyar SLPP, su ka shirya, a harabar hukumar zaɓe mai zaman kanta, domin nuna adawa da wannan sakamako.

Ɗan takaran SLPP ,mataimakin shugaban ƙasa mai ci yanzu, Solomon Barewa, ya zargi hukumar zaɓen da kasancewa karyar farautar jam´iyar adawa.

To saidai masu sa ido, daga ƙasashen ƙetare, sun ce zaɓen ya wakana cikin matakan adalci.