Jirgin yaki ya kashe fararen hula a Siriya | Labarai | DW | 09.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin yaki ya kashe fararen hula a Siriya

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Siriya sun tabbatar da mutuwar fararen hula 21 ciki har da kananan yara bayan da jiragen yakin Amirka suka kaddamar da sumame kan kungiyar IS a gabashin kasar.

Jiragen Amirka sun kaddamar da hare-haren ne a birnin Raqqa da ke zama sansanin mayakan IS a gabashin Siriya. Sai dai dakarun kawancen da ke yaki a kasar na kokwanto a kan adadin fararen hula da kungiyoyin sa ido ke cewa jiragensu na kashewa. Amma a baya-bayannan sojojin sun sha alwashin taka tsantsan na kauce wa jefa bama-bamai da ke halaka fararen hula da sunan farautar 'yan ta'adda.

A cikin makonnan ne dai dakarun suka datse babbar hanya da ta hada birnin Raqqa da yankin Deir al-Zor da ke zama mafakan 'yan awaren Siriyan. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun kawancen Amirka suka tabbatar da karin wasu sojoji 400 da motocin atilari da sauran makaman yaki da nufin fatattakar kungiyar IS a birnin Raqqa na kasar Siriyar.