1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin saman Flydubai

Salissou BoukariMarch 19, 2016

Wani jirgin sama samfirin Boeing 737 dauke da fasinjoji 55 da kuma ma'aikatan jirgin guda bakwai ya fadi a birnin Rostov na kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/1IGJ0
Symbolbild Passagiermaschine in Russland abgestürzt
Hoto: Reuters/A. Jadallah

Rahotanni dai na cewa babu ko mutum guda da ke cikinj jirgin da ya tsira da ransa. Jirgin dai ya taso ne daga birnin Dubai, a cewar ministan harkokin agaji na kasar ta Rasha Viktor Ianoutsenko jirgin ya fadi da wajejan shabiyun daren wannan Asabar din, dauke da fasinjoji 55. Daga cikin fasinjojin dai mata 33 ne kana maza 18 da kuma yara kanana guda hudu. Mutune 44 daga cikinsu 'yan kasar Rasha ne, takwas 'yan kasar Ukraine, biyu 'yan kasar Indiya, da mutun guda dan kasar Azarbaijan da kuma ma'aikatan jirgin guda bakwai."

Tuni dai shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya isar da gaisuwar ta'aziya zuwa ga iyallan mamatan, yayin da kwamitin bincike ya sanar cewa ya soma gudanar da bincike na manyan laifuka da ke da nasaba da saba ka'idojin tsaro da kuma tafiyar da ingancin filin sauka da tashin jiragen sama. A cewar gidan talbijin na LifeNews jirgin dai ya fadi ne a nisan mita a kalla 100 da inda ya kamata ya sauka.