1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin saman Fasransa ya yi sabkar gaggawa a Mombasa

Gazali Abdou TasawaDecember 20, 2015

Jirgin wanda ya taso daga tsibirin Moritiyas dauke da fasinjoji 459 ya yi saukar gaggawa a birnin na Mombasa na Kenya bayan da aka gano wani kunshi a cikin bandakin jirgin da aka yi zaton bam ne.

https://p.dw.com/p/1HQd1
Kenia Boeing 777 Air France Flug Notlandung
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani jirgin jigilar fasinja na kamfanin Air France ya yi saukar gaggawa a daran Asabar washe garin wannan Lahadi a birnin Mombasa na kasar Kenya bayan da aka gano wani kunshi da ba a yarda da shi ba a cikin jirgin wanda ya taso daga tsibirin Moritiyas zuwa birnin Paris dauke da fasinjoji 459.Hukumar 'yan sandar kasar ta Kenya wacce ta bayyana wannan labari ta ce jirgin ya nemi izinin saukar gaggawa bayan da aka gano wani kunshi a cikin bandakinsa da ake zaton Bam ne.

Tuni dai aka tura da jami'an hukumar 'yan sanda masu yaki da aiyyukan ta'addanci kwararru a fannin kwance domin binciken kunshin dama jirgin baki daya.