Jirgin saman Amirka mai saukar ungulu ya fadi a Iraqi | Labarai | DW | 08.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin saman Amirka mai saukar ungulu ya fadi a Iraqi

Wani jirgin saman Amirka mai saukar ungulu ya yi hadari a Iraqi, inda dukkan mutane 12 dake ciki suka rasa rayukansu. Sannan wasu sojojin Amirka 5 sun mutu a jerin hare hare da aka kai a yammacin kasar ta Iraqi. Wata sanarwa da rundunar sojin Amirka ta bayar a yau lahadi ta ce alikoptan ya fado ne a wani wurin da babu jama´a dake arewacin Iraqi jim kadan kafin karfe 12 dare. Cikin wadanda suka mutu a wannan hadari akwai matukan jirgin saman 4 da fasinjoji 8. Sojin Amirka sun ce suna gudanar da binciken gano musabbabin aukuwar hadarin, kuma ba su sani ba ko harbo alikoptan aka yi. A wani lamarin kuma an halaka sojojin Amirka 5 a ciki da wajen birnin Falluja. Sannan wasu ´yan bindiga da suka yi garkuwa da wani dan Faransa sun sake shi a birnin Bagadaza, yayin da sojojin Amirka kuma suka kai samame a ofisoshin wata kungiyar ´yan Sunni mai fada a ji, don mayar da martani akan abin da sojin Amirka suka kira alakar kungiyar da hare-haren ta´addanci.