1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin sama da 'yan wasa daga Brazil ya fadi

Masu aikin agaji tuni sun fara kwashe mutanen da suka rayu daga wurin da hadarin ya afku a kasar ta Kwalambiya ciki kuwa har da 'yan kwallon kafa daga Brazil.

Wani jirgin sama dauke da mutane 81 ciki har da wata tawagar kwallon kafa daga Brazil ya yi hadari a kasar Kwalambiya kamar yadda ma'aikatar da ke lura da  zirga-zirgar jiragen sama a kasar ta bayyana a ranar Talatan nan.

Masu aikin agaji tuni sun fara kwashe mutanen da suka rayu daga wurin da hadarin ya afku, kuma a cewarsu cikin wadanda lamarin ya ritsa da su akwai tawagar kwallon kafa ta Chapocoense daga Brazil cikin fasinjoji 72 da ma'aikatan jirgin tara.