Jirgin ruwan yahudawa ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza
September 26, 2010Talla
Ƙungiyoyin yahudawa 'yan fafutukar kare haƙƙin bil'adama da
Isra'ila da Turai da kuma Amirka sun cika kayan agaji ga wani
jirgin ruwa domin kaiwa falasɗinawa da ke zirin Gaza, a
ƙoƙarin da su ke yi na karya shingen da Isra'ila ta sanyawa
masu muradin zuwa yankin. Tuni dai jirgin kayan agajin ya
bar ƙasar Cyprus ɗauke 'yan fafutuka takwas ciki har da
matuka jirgi ukku da kuma 'yan jarida biyu. Wani bayahuden
da ya tsira daga kissan kiyashin Nazi da aka yiwa yahudawa
mai suna Reuven Moskovitz - ɗan shekaru 82 da haihuwa, ya
ce wani nauyi ne da ya rataya a wuyansa, a matsayin wanda
ya tsira daga wancan zaluncin, ya nuna adawarsa ga abinda
ya kira kisa, da cin zarafi da kuma sanya al'ummar Gaza cikin
fursuna ciki kuwa kamar yadda ya ce har da mata da ƙananan
yara da yawan su yakai dubu 800. Shi kuwa Yonatan, wanda
kamar Moskovitz ke cikin jirgin, ya ce ba wai suna son yin fito
- na - fito ne da Isra'ila ne ba, amma idan sojojin Isra'ila suka
dakatar da jirgin, to kuwa ba za su taɓa ƙyalesu kai jirgin
zuwa bakin tekun Ashdod ba, inda suka karkatar da akalar
sauran jiragen da ke ɗauke kayan agaji ga al'ummar Gaza.
Jirgin ruwan dai zai yi tafiya mai nisan sa'oi 36 ne kafin zuwa
yankin na Gaza. Ministan kula da harkokin tsaron Isra'ila Ehud
Barak ya sha nanata cewar Isra'ila za ta ƙwace duk wani jirgin
da ya zo kusa da Gaza, yankin da Ƙungiyar Hamas ce ke da
iko da shi.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Yahouza Sadissou Madobi
Talla