1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain za ta karbi jirgin ruwan Aquarius

Abdourahamane Hassane
June 11, 2018

Yanzu haka wani jirgin ruwa na ceton 'yan cirani Aquarius na wata kungiya mai zaman kanta ta Faransa na jiran samun izini don isa a gabar ruwan tekun wata kasa don sauke bakin hauren da yake dauke da su.

https://p.dw.com/p/2zIO1
Italien Sizilien Flüchtlinge auf dem Schiff Aquarius im Hafen von Catania
Hoto: Reuters/G. Mangiapane

Hakan kuwa ya biyo bayan da kasashen Malta da Italiya suka hana jirgin isa a gabar tekunsu. Jirgin ruwan wanda ke tsakanin Malta da Italiya na dauke da 'yan cirani sama da 600 da aka ceto daga gabatar tekun Libiya.