Jirgin ruwa ya nutse a Siera Leone | Labarai | DW | 04.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin ruwa ya nutse a Siera Leone

A ƙasar Siera Leone, ana ci gaba da laluben mutane da su ka ɓata a sakamakon nutsewar wani jirgin ruwa shake da jama´a a cikin teku.

Ya zuwa yanzu an tabbatar da cewar, mutane 58 su ka rasa rayuka, 2 su ka ƙetara rijiya da baya, a yayin da kuma masu ceto, ke ci gaba da laluben sauran.

Shugaban tashar jirgin ruwa Freetowen ya nunar da cewa, mutane kusan 150 ne su ka yi kasa ko bisa.

Wannan shine haɗari mafi girma da ya wakana a dunia, tun bayan wanda ya hadasa assara rayuka fiye da dubu, a cikin ruwan maliya, bayan wani jirgin ruwa ya nutse cikin kogin Maliya, a kann hanyar sa ta zuwa Saudi Arabia daga Masar a sheakara da ta gabata

Hatsarin jirgin ruwa mafi muni kuwa, shine na ƙasar Senegal a shekara ta 2002 wanda ya hadasa mutuwar mutane kussan dubu 2.

A game da haɗarin na Siera Leone, hukumomin ƙasar, sun alƙawarta gudanar da bincike, domin tantance mussabbabin sa.