1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin-ruwa mafi girma a Duniya

Abba BashirFebruary 20, 2006

Takaitaccen bayanin Jirgin-ruwa mafi girma a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVX
Jirgin-ruwan Cargo Vessels
Jirgin-ruwan Cargo VesselsHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon, ta fito ne daga hannun Malama Zahara’u Na-dabo mazauniya a Jidda ta kasar Saudiyya. Malamar tace , Ni dai a sani na Titanic shine jirgin Ruwa mafi girma a Duniya kafin ya yi hatsari ya nutse a cikin teku. To yanzu bayan halakar Titanic, wane jirgin Ruwa ne mafi girma a Duniya, kuma ta yaya zaa iya kwatantashi da Titanic?

Amsa : To a yau dai ba a gobe ba , rukunin Jiragen ruwa da ake kira da suna (cargo vessels) sune Jirage mafiya girma a Duniya .Kuma kamfanin da ake kira da suna (oil tanker Jahre Viking) su ne suke kera irin wannan Jirgi.

Jirgin Ruwan na cargo vessels dai ya na da tsawon da ya kai kafa 1503, sannan kuma fadinsa yakai kafa 226. Har’ila yau kuma yana da nauyin da ya kai Ton 565,000 wato dai kamar nauyi buhun hatsi 5,650,000. kenan.

To ta bangaren kwatankwaci da Titanic, shi taitanic tsawonsa kafa 883 ne, fadinsa kuma kafa 93 ne, sannan kuma ya da nauyin Ton 45,000.Shi dai Jirgin Titanic yakan dauki mutane 3,500 wadanda suka hada da fasinja da kuma kungiyar ma’aikatan Jirgi,amma kuma yawan kwale-kwalen da ya kann iya dauka domin tserar da rayukan mutane ida wani hatsari ya auku,basu wuce geda 1000 ba.

Jirgin ruwan dai na Titanic, ya gamu da ajalinsa ne sakamakon tunkuyar wani tsauni na kankara da ya yi a cikin teku a ranar 14 ga wata Aprilun 1912, da misalin karfe 11: 40 na dare.

Sannan kuma an tabbatar da cewa mutane 2,228 ne a cikin jirgin lokacin da ya tunkuyi tsaunin kankarar,kuma daga cikinsu mutane 705 ne kawai suka tsira da ransu.amma sauran mutane 1,523 sun nutse ne ko kuma sun kankare sun mutu acikin daskararren ruwan tekun.