Jirgin ruwa ɗauke da kayan agaji ya doshi Gaza | Labarai | DW | 11.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin ruwa ɗauke da kayan agaji ya doshi Gaza

Duk da haramcin da Isra´ila ta yi jirgin ruwan Libiya shaƙe da kayan masarufi ya darkaka zuwa zirin Gaza

default

Jirgin ruwa da kayan agaji daga Libiya ya darkaka zuwa Gaza

Wani jirgin ruwa shaƙe da abinci na kan hanyar sa zuwa zirin Gaza.

Gidauniyar agaji ta Ƙhadafi ce, mallakar ɗan shugaban ƙasar Libiya Seif Al-Islam ta yi hayar wannan jirgin ruwa, domin kai taimako ga al´umomin Gaza dake cikin halin uƙuba.

To sai dai hukumomin Isra´ila sun umurci matuƙa jirgin, kar su kuskura su shiɗe kayan a tashar jiragen ruwan Gaza. Ministan tsaro Ehud Barak,ya buƙaci a sauke wannan kaya, au a tashar jiragen ruwan Isra´ila ta Ashdod, ko kuma ta Al-Arish a Misira.

Amma a nata ɓangare Gidauniyar agaji ta Ƙaddafi ta ce sai ta ga abinda ya turewa buzu naɗi, kuma a yanzu haka ta na ci gaba da darkakawa zuwa tashar jiragen ruwan Gaza.

Idan dai ba a manta ba, a ƙarshen watan Mayu, Isra´ila ta kai hari ga wani jirgin ruwa mallakar Turkiyya a kan hanyar sa zuwa Gaza, inda mutane da dama suka rasa rayuka.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Ahmed Tijani Lawal