Jirgin kasa ya kashe mutane 33 a Kwango
November 13, 2017Talla
Jirgin kasan ya fada wani rami ne a yayin da yake kokarin haura wani tudu a kan titin birnin Lubumbashi birnin na biyu mafi girma a kasar zuwa Luenana, inda jirgin ya dauko tankokin mai 13da suka fashe suka haddasa gobara nan take bayan subuce wa zuwa rami.
A baya ansha samun hatsarin jiragen kasa a yankin Luena, kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross tace akalla mutane mutane sama da dari sun mutu yayin da wasu sama da mutane 160 suka jikkata a wani hatsarin jirgin kasa da ya kife a shekarar 2014.