Jirgi a Pakistan ya yi hadari da mutane 47 | Labarai | DW | 07.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgi a Pakistan ya yi hadari da mutane 47

Jirgin saman na PIA mai lamba PK661 ya yi hadari a lardin Pakhtunkhwa kamar yadda hukumomin suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wani jirgin sama mallakar kasar Pakistan dauke da fasinja 47 ya yi hadari a ranar Laraban nan yayin da yake kan hanyarsa tsakanin birnin Chitral na Arewacin kasar zuwa Islamabad kamar yadda mahukuntan da ke lura da harkokin sufurin jiragen sama suka bayyana a kasar.

Masu aikin agaji dai sun bayyana cewa kawowa yanzu mutane 36 ne suka rasu ana kuma sa ran adadin zai karu. Karamin jirgin dai mai suna ATR-42 ya fadi ne a garin  Hawalian a Arewacin Pakistan, garin da ked a tazarar kilomita 75daga Areawacin babban birnin kasar ta Pakistan.