1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiran sakamakon zaben shugaban kasa a Gabon

November 28, 2005
https://p.dw.com/p/BvJ1

A kasar Gabon a na ci gaba da jiran sakamakon zaben shugaban kasa, da aka gudanar jiya.

Baki daya runfunan zabe kussan dubu ne su ka buda a fadin kasar da kuma ketare, inda mutane kimanin dubu dari da ya cencenta su kada kuri´u.

Saidai masu kulla da zaben, sun shaida cewa mutane kalilan su ka hito, domin kada kuri´un su.

Wannan halayen ko in kulla da jama´a ta nuna, ba zai rasa nasaba ba, da tunanin cewar, ko kamin a bayyana sakamakon, an riga an san wanda zai lashe zaben, wato shugaba mai ci yanzu Omar Bango.

A halin da ake ciki, shugaba Bango,dan shekaru 69 a dunia,shine shugaban Afrika, da ya fi dadewa bisa karagar mulki,bayan ya share shekaru 38,ya na jan ragamar kaasar Gabon.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta nunar cewa, za a bayyana sakamakon karshe, na da yan kwanaki masu zuwa, ta kuma tabbatar da an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali a fadin kasar baki daya.