Jiran sakamakon zaben shugaban kasa a Burkina Faso
November 14, 2005Talla
A kasar Burkina Faso an kammala zaben shugabn kasa lami lahia.
A halin da ake ciki a na shiga jiran sakamako.
Saidai hukumar zabe mai kanta ta sanar cewa duk da fara kidayar kuri´u da a ka yi ba za a samu sakamakon ba sai nan da kwanaki 3 masu zuwa.
Tunni sarkin yakin zaben jam`iyar CDP ta shuga Blaize Kompaore ya shaidawa manema labarai cewa dan takara su za shi lashe zaben tun zagaye na farko, da kashi 65 zuwa 70 na yawan kuri`un da a ka jefa.
Wakilan kungiyar tarayya Afrika sun yabawa zaben tare da bugun gaban cewa wata shaide ce mai nuna Demokradiya ta nuna a kasar Burkina Faso.
Sun kuma tabatar da an gudanar da zaben cikin adalci da ta kamata.