Jiran sakamakon zaɓe a Jamhuriya Demokradiyar Kongo | Labarai | DW | 01.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiran sakamakon zaɓe a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

A jamahuriya Demokradiyar Kongo, a na cikin jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki ,da a ka shirya ranar lahadi da ta wuce, a faɗin ƙasar baki ɗaya.Ya zuwa yanzu hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta ƙirga fiye da kashi 50 bisa 100, na ƙuri´un da aka kaɗa, saidai ba a za a samu sakamakon ƙarshen ba, sai nan da, a ƙalla makwani 3 masu zuwa.

Idan akwai buƙatar zagaye na 2,a zaɓen shugaban ƙasa, za gudana ranar 29 ga watan oktober.

Ƙasashe, da ƙungiyoyin na dunia, sun yi yabo da jijina, ga al´ummomin wannan ƙasa, a game da dattako da halin girma, da su ka nuna, ta hanyar shirya zaɓe mai tsabta , cikin kwanciyar hankali da lumana.

To saidai wasu masharahanta, na nunar da cewa, kar ayi saurin yaban ɗan kuturu, domin komai na iya faruwa wajen bayana sakamakon zaɓen.

A dangane da haka, tabbatar da zaman lahi Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ya dangata da yadda yan takara zaɓen shugaban ƙasa, za su amince, ko watsi da sakamakon zaɓen.

Don haka ne ma, ƙungiyar gamayya turai, ta yi kira ga yan takara, da su amince da sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta zata bayyana.

EU ta yi imani cewar, an gudanar da zaɓen, ba tare da maguɗi ba, kuma sakamakon da zai hito, zai yi daidai da buƙatar jama´a.