1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiran sakamakon zaɓen Cote d'Ivoire

November 29, 2010

Jami'an tsaro biyar suka mutu a zaɓen da ya gudana a ranar Lahadi

https://p.dw.com/p/QLL6
Mutane a layin jiran jefa ƙuri'a a ƙasar Cote d'IvoireHoto: AP

Yanzu haka al'ummar ƙasar Cote d'Ivoire tana can tana jiran sakamakon zaɓen fidda gwani, da ya wakana a ranar Lahadin da ta shuɗe, inda aka fafata tsakanin shugaban ƙasar mai ci yanzu Laurent Gbagbo da tsohon Faraminista kuma tsohon mataimakin shugaban Asusun Lamuni na Duniya Alassane Watara, sai dai jami'an tsaro 5 sun mutu a lokacin da wannan zaɓen ke wakana.

Zuwa wannan lokacin, hukumar zaɓen ƙasar ta Cote d'Ivoire ba ta soma wallafa sakamakon dake hannun ta ba na zaɓen, ko da yake sai nan zuwa ranar Laraba ake tsammanin samun wataƙila ɗaukacin sakamakon wannan zaɓen da koke-koke suka mamaye ƙarshensa.

Domin ɓangaren Alassane Watara ya koka ne game da abinda ya kira matsin lambar da aka yiwa magoya bayansa a waɗansu wurare a cikin garin Abidjan da ke yamma maso tsakiyar ƙasar, yayin da ɓangaren Laurent Gbagbo ya koka game da abin ya ce hana magoya bayan sa jefa ƙuri'a a arewacin ƙasar, inda ma shugaban yaƙin neman zaɓensa ya ce za su nema hukumar zaɓe da ta soke zaɓen wannan yakin.

Jami'an tsaro biyar ne, suka rasa rayukansu a Dalowa a yammacin ƙasar a daidai lokacin da aka kammala zaɓen, kuma sun rasu ne a wata husata da waɗansu suka nuna a lokacin da suke zargin an hana su gudanar da 'yancinsu na 'yan ƙasa.

Su dai magoya bayan Alasane Watara, sun alaƙanta wannan halin da ake ciki ne, da matakin da shugaban ƙasar Laurent Gbagbo ya ɗauka na kafa dokar hana yawon dare, tun daga ranar Lahadi izuwa Laraba mai zuwa, abin da ya sa 'yan adawar cewa ɗaukar wannan matakin manufa ce ta yin maguɗin zaɓe, yayin da faraministan ƙasar ke cewa shugaban ƙasar bai shawar ce shi ba kamin ya ɗauki wannan matakin, kuma ko a yau da safe waɗansu sanarwoyi da suka ci karo da juna tsakanin ma'aikatar ministan cikin gida da ke ƙarƙashin fadar shugaban ƙasar, da fadar faraminista, na farko ya nuna cewa zaɓen bai inganta ba a arewacin ƙasar, yayin da fadar faraministan ke cewa bata da wannan labarin, abin da ke bayyana a hilin irin banbance banbancen ra'ayi dake tsakanin ɓangarorin guda biyu game da wannan zaɓen.

A cewar Herr Dermot wakilin Tarayyar Turai a wajen sa ido a zaɓen, rasa rai da a ka samu abin takaici ne.

"Ina nuna alhini na, game da rashe rashen rai da aka samu a Abidjan a lokacin waɗansu arangama, tare da fatan irin waɗannan ababen ba za su sake aukuwa ba bayan kammala wannan zaɓen."

Mutanen da suka fito domin jefa ƙuri'a ba su kai kwatankwacin waɗanda suka yi hakan ba a zagaye na farko.

Wata mata da ta jefa ƙuri'a ta nuna gamsuwar ta game da yadda zaɓen ya gudana.

"Komi ya wakana a cikin tsari, kowa ya jira lokacin da zai jefa ƙuri'a, babu turereniya, komi ya gudana yadda ya kamata, kuma mun yi komi cikin ƙa'ida."

Har izuwa wannan lokacin dai ba sakamako ko guda da hukumar zaɓen ƙasar ta wallafa, kuma ganin cewa 'yan ƙasar na cikin jira, wannan na ci gaba da ƙara sasu a cikin marmarin sanin yadda za ta kaya tsakanin 'yan takarar guda biyu.

Mawallafi: Harouna Mamane Bako

Edita: Mohammad Nasiru Awal