1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamid kan gaba a sakamakon zaɓen wucin gadi a Afganistan

September 4, 2009

Harmid Karzai ke gaba a sakamakon wucin gadin zaɓen shugaban ƙasar Afganistan, saidai yanzu hukumar zaɓen ƙasar Afganistan ta ƙasa bayyana sakamakon ƙarshe.

https://p.dw.com/p/JSRf
Hamid Karzai na kan gaba a sakamakon wucin gadin zaɓen AfganistanHoto: AP

A ƙasar Afganistan ana ci gaba da kidaya ƙuri´un zaɓen shugaban ƙasar a daidai lokacin da ake ci gaba da tashin hankali da aka saba fuskanta. A ma ci gaba da tashin hankali a yau an fuskanci asarar rayukan mutane kimanin 56 a lardin Kundus sakamakon tashin bama-bamai daga wasu tankokin jigilar man fetur guda biyu a baya ga wasu su 23 da suka mutu a wani hari na kunar baƙin wake. A dai halin da ake ciki shugaba Hamid Karzai mai ci yanzu ya samu kashi kashi 47 da ɗigo uku daga cikin dari na sakamakon ƙuri´un da hukumar zaɓen ƙasar ta bayar.

A dai halin da ake ciki yanzu babu abin da ke ɗaukar hankalin alumar Afganistan illa tarurrukan manema labarai da ake gudanarwa game da zaɓen shugaban ƙasar a Kabul babban birnin ƙasar. Hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta dai ,tana ba da sakamakon zaɓen daki-daki bayan kowane kwana biyu ko ukku. Ya zuwa yanzu dai an gama ƙidaya ƙuri´un da aka kaɗa a kashi 60 daga cikin ɗari na runfunan zaɓen.

A sannu a hankali dai shugaba Hamid Karzai na kan hanyar samun kashi 50 daga cikin ɗari da ɗoriya na sakamakon zaɓen da yake bukata domin kauce wa zagaye na biyu. Bisa ga dukan alamu dai, Karzai zai iya samun nasara ganin cewa har yanzu ba a gama ƙidaya ƙuri´u daga kudancin ƙasar dake zaman makarfafa ga gare shi ba. To sai kuma ayar tambaya anan ita ce ko zai iya yin haka ta halaltaiyar hanya.Akan haka Abokin hamayyarsa Abdullah Abdulaah yayi tsokaci yana mai cewa:

In da a ce a wata guda da ya wuce ka tambayani ko shin zan yarda da samun nasarar Karzai da na ce maka ei ba da wata wata ba. Amma da yake yanzu ni da sauran alumar Afganistan mun shedar da irin maguɗin da aka tafka a wannan zaɓe to kenan muna bukatar ganin an bi halatacciyar hanyar. Karzai ba zai samu nasara ba in har ya kauce wa wannan hanya

Abin da Abdullah ke nufi da bin halataciyar dai a fili yake. A dai halin da ake ciki hukumar amsar karraraki ba ta gama bincike akan kararrki sama da 2000 da aka mika mata ba. Kuma guda dari daga cikinsu kararraki ne da ke bukatar kulawar gaggawa.kuma hakan abu ne da zai yi tasiri akan sakamakon zaɓen. Abdullah yayi misali da wata gunduma da babu ko runfunar zaɓe guda da aka buɗe a cikinta.

Yace akwai wata gunduma da ba a buɗe ko runfunar zaɓe ɗaya a cikinta ba.Amma kuma sakamakon da aka bayar ya bayyanar da kaɗa dubban ƙuri´u a wannan gunduma alhalin kuwa babu inda aka jefa ƙuri´a a wannan wuri. To kenan an cike akwatunan zaɓe ne da ƙuri´u na jabu.

A haƙiƙa dai kwanaki kaɗan bayan zaɓen sai da yan sa ido suka yi ƙorafin cike akwatunan zaɓe da ƙuri´u na jabu. A yanzu dai ´yan sa idon suna jira ne su ga irin matakin da hukumar ƙarrarakin zaɓen za ta ɗauka. Kuma ko shakka babu, duk wata gwamnati da za a kafa a kasar ta Afganistan ta hanyar maguɗi za ta fuskanci matsala daga ´yan Taliban.

Mawallafi: Halima B Abbas

Edita: Awal N. Awal