1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen Saudiyya sun halaka mutane 140 a Yemen

October 9, 2016

MDD ta tabbatar da mutuwar mutane sama da 140 a birnin Sana'a na Yemen a cikin wasu hare-hare ta sama da jiragen yakin kawancen kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen suka kai kan wani taron zaman makoki.

https://p.dw.com/p/2R2yT
YEMEN-CONFLICT-SANAA-STRIKES
Hoto: AFP/Getty Images


Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da mutuwar mutane sama da 140 a yayin da wasu 525 suka ji rauni a Yemen a ranar Asabar a cikin wasu hare-hare ta sama da jiragen yakin rundunar kawancen kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin kasar Yemen suka kai kan wani taron zaman makoki a Kudancin babban birnin kasar na Sana'a. 

Tuni dai Amirka abokiyar kawancen Saudiyyar ta yi tir da Allah wadai da kai wannan hari tare da sanar da sake yin nazari kan goyon bayan da take bai wa Saudiyya a yakin na Yemen. Sai dai kuma mahukuntan kasar Saudiyyar sun ce ba su da hannu a cikin afkuwar wannan lamari, kuma sun amince Amirkar ta shiga jerin wadanda za su gudanar da bincike a kai. 

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka taba fuskanta a kasar ta Yemen tun bayan da rundunar kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin kasar ta kudiri aniyar korar gwamnatin 'yan tawayen Houthi da nufin sake maido da gwamnatin Shugaba Abd Rabbo Mansour Hadi kan karagar mulkin kasar.