1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen saman yakin Isra´ila sun ragargaza wani bene a birnin Tyre

Jiragen saman yakin Isra´ila sun lalata ofisoshin kwamandan Hisbollah dake birnin Tyre na kudancin Libanon. Ko da yake babu kowa cikin ginin a lokacin da aka kai harin amma mutane 12 ciki har da kananan yara dake kusa sun jikata. Fashewar wasu abubuwa guda biyu ya ta da bakin hayaki da ya tirnike tsakiyar birnin na Tyre yayin da aka samu katsewar wutar lantarki a wasu wurare na birnin. An kai harin ne akan wani bene mai hawa 7 dake kunshe da ofisoshin Sheikh Nabil Kaouk kwamandan Hisbollah a kudancin Lebanon.