Jiragen saman yakin Isra´ila sun koma ga kai hare hare akan Lebanon | Labarai | DW | 11.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen saman yakin Isra´ila sun koma ga kai hare hare akan Lebanon

Majiyoyin asibiti a arewacin Lebanon sun ce an kashe fararen hula 11 sannan aka jikata wasu 9 a wasu hare hare da jiragen saman yakin Isra´ila suka kai kan wata gada da sanyin safiyar yau juma´a. Hakazalika jiragen saman yakin Isra´ila sun sake kai hare hare akan unguwar Dahiyeh da ya kasance matattarar mayakan Hisbollah a kudancin Beirut. A jiya wani jirgin saman Isra´ila ya jefa kasidu dake kira ga mazauna yankin da su gaggauta ficewa daga unguwar ta ´yan shi´a. Da farko dakarun Isra´ila sun ce sun kwace garin Marjayoun mai muhimmanci na mabiya darikar Kirista. A kuma can arewacin Isra´ila mutane biyu sun rigamu gidan gaskiya a wani harin roka da Hisbollah ta harba daga Lebanon ya sauka kan wani kauyen larabawa. A kuma halin da ake ciki babban jami´in dake kula da ayyukan jin kai na MDD, Jan Egeland ya soki lamirin Isra´ila da Hisbollah da kawo cikas ga tura agaji zuwa kudancin Lebanon. Rahotanni sun nunar da cewa asibitoci a kudancin Lebanon na fuskantar karancin abinci, makamashi da kuma magunguna.