Jiragen Israila na ci gaba da kai hari Gaza | Labarai | DW | 30.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen Israila na ci gaba da kai hari Gaza

Jiragen saman yakin Israila sunci gaba da da hare hare yankin Palasdinawa inda da safiyar yau suka jefa bam akan maaikatar harkokin cikin gida ta a birnin Gaza,a kokarinsu na tilastawa yan gwagwarmaya na Palasdinawa su sako sojan da suka yi garkuwa da shi,yayinda kuma masu shiga tsakani larabawa suke ci gaba da kokarin kawo karshen rikicin.

Yayinda hare haren da Israila take kaiwa kann Palasdinwa ya shiga kwana na uku,shugaban kasar Masar Hosni Mubarak yace an kusa cimma nasara na sako sojan,amma Israila tace bata yarda da sharuddan da aka mika ba.

Jamian Israilan sun baiyana cewa,basu da masaniya akan wasu sharuda kuma basu da shirin tattaunawa da wadanda suka kame sojan.

Sai dai kuma Israilan ta dakatar da shirinta na mamaye arewacin Gaza.

A yau din nan ne kuma jamian Palasdinawa suka baiyana mutuwar wani dan kungiyar Islamic Jihad sakamakon rauni da ya samu a lokacin harin Israila ta kai a Rafah.