1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jimami a Somaliya bayan harin ta'addanci

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 22, 2018

Kimanin mutane 14 ne suka hallaka yayin da wasu 10 kuma suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota a ksar Somaliya.

https://p.dw.com/p/2uoKM
Harin kunar bakin wake a Somaliya
Harin kunar bakin wake a SomaliyaHoto: picture-alliance/AA/S. Mohamed

Mahukuntan kasar ta Somaliya dai sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran wadanda  harin da aka kai a kusa da Otal din Weheliye da ke kan titin Makka Almukarramah a Mogadishu babban birnin kasar ya rutsa da su. Dama dai hanyar ta kasance wadda ke yawan fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar masu kaifin kishin addini ta al-Shabab da ke zaman mafi hadari a nahiyar Afirka, wadda kuma ta addabi Somaliyan. Tuni ma dai kungiyar ta al-Shabab ta dauki alhakin kai wannan harin.