Jill Carroll ta iso Jamus akan hanyarta ta zuwa gida | Labarai | DW | 01.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jill Carroll ta iso Jamus akan hanyarta ta zuwa gida

Kwanaki biyu bayan sako yar jaridar nan dake da asali a Amurka daga garkuwar da akayi da ita a Iraqi, a yanzu haka ta iso tarayyar Jamus.

Jill Carroll, wacce ta shafe kwanaki 82 a hannun wadanda suka yi garkuwar da ita, ta iso kasar ta Jamus ne a cikin koshin lafiya.

A wani hoton bidiyo da aka nuno Jill Carrol, kafin sako ta ta yabawa wadanda suka yi garkuwa da itan tare da sukar lamirin Amurka na afkawa da Iraqi da yaki.

Iyaye da yan uwan yar jaridar sun shaidar da cewa, tursasawa yar jaridar akayi tayi ire iren wadan nan kalamai, wanda a cewar su na daga cikin sharudan sako ta.