Jihar NRW zata shiga dangantakar hadin gwiwa da kasar Ghana | Zamantakewa | DW | 23.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Jihar NRW zata shiga dangantakar hadin gwiwa da kasar Ghana

Akokarinta na taimakawa kasashe masu tasowa Jihar NRW dake jamus zata kulla dangantaka da Ghana

Ministan kula da Iyali da hadin kan kasa na NRW,Armin Laschet

Ministan kula da Iyali da hadin kan kasa na NRW,Armin Laschet

Gwamnatin jihar Nordrhein Westfalen dake nana tarayyar jamus ta gabatar da sabbin manufofinta danagane da ayyukan hadin gwiwa da bada tallafi wa kasashe masu tasowa.

Maaikatar kula da harkokin sadarwa da iyali da mata da hadin kan kasa ta shirya wannan wannan mahawar da akayai a birnin Dusseldorf dake zama babbar headquatar wannan jiha data hada manyan birane da dama a nan jamus.

An dai gabatar da sabbin tsare ztsare da munufofi da gwamnatin wannan jiha ta sanya a gaba domin ganin cewa an anyi aiki kafada da kafada wajen cimma na anasaran aiwatar dasu,wadanda tun daga shekarata 1993 aka kudiri aiwatar dasu.

Sabbin manufofin dai sun kunshi batutuwa guda 10,wadanda suka hada da cimma manufofin da mdd ta sanya gaba wajen rage talauci ta hanyar samarda yanayin dangantaka na taimakekeniya,domin cigaba,da kulla dangantakara aiki kafada da kafada tsakanin gwamnatin jihar N/R dada kungiyoyin bada taimakaon raya kasashe na cikin jamus da kuma ketare da wasu cibiyoyin addinin krista da kungiyoyi masu zaman kansu dake cikin jihar,musamman ma amatsayin wannan jiha dake za,ma wadda ke zama cibiyar majalisar dunkin duniya.

Akasarin wadannan manufofi dai zasu fi yin tasiri ne akasashenmu na Afrika masu tasowa da suka hadar da kasar Ghana kamar yadda ministan hadin kan kasa anan jihar Nordrhein westfalen,Armin Laschet yayi bayani…...

“Muna fatan cimma wadannan sabbin manufofi da muka sanya buri akansu adangane da aiki tare domin cimma nasara.Manufar hakan kuwa shine amfani da irin basirar da Alla ya huwacewa baki wadanda ke zaune a wannan jiha ta NordRhein ,wadanda suka fito daga Afrika,musamman kuma kasar Ghana,adangane da irin fasaha da Allah ya huwace,da kuma ababan da sukeyi da kudaden da suke aikawa kasashensu.

Ministan hadin kaan kasar yace akwai kimanin yan kasasr ta Ghana 9.000 dake sassa daban daban na wannan kasa,kuma kusan rabinsu suna da takardar Pasport na shedar dan kasa ta jamus,abunda zaa iya bayyanawa da ingantaccen wakilcin kasar anan tarayyar jamus.

Armin Laschet yace wadannan tsare tsare da manufofi da muka sanya gaba kazalika nada nufin samarda ingantattun yanayi na danghantaka daga gudummowa na son daga majamiu,da kungiyoyi zuwa kasar Ghana.Domin Ghana ta zame abar misali a nahiyar Afrika,saboda tsari da take dashi cikin harkokin tattalinta,da bin dokokin na sakarwa harkokin kasuwanci mara ,a hannu guda kuma ga gindion zama da mulkin democradiyya ya samu ,wanda hakan ne ya sanya Ghana ta zame kasar fata da alfahari a garemu”