1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jihar Dkota a Amurka ta zartar da sabuwar doka

Gwamnan jihar Dakota a Amurka daya fito daga jamiyyar Republican, ya saka hannu kann wata doka data hana zubar da ciki a duk fadin jihar baki daya.

Rahotanni sun nunar da cewa dokar ta kuma amince da´a zubar da cikin ne kawai , idan hakan zai taimaka wajen kobuto rayuwar wacce za´a zubarwa.

Bayanai dai sun nunar da cewa da alama wannan kuduri na´a matsayin hannun ka mai sanda ne ga mahukuntan na Amurka na duba yiwuwar gudanar da kwaskwarima ga dokar data bayar da ikon zubar da ciki a kasar ta shekara ta 1973.

Ya zuwa yanzu dai masu fafutikar hana zubar da ciki a kasar na fatan cewa nan bada dadewa ba, alkalan kotun koli da shugaba Bush ya nada a kwana kwanan nan , zasu dauki matakan ganin an soke wannan doka.