1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jihadil Islami ta ɗauki alhakin hari a kan sojojin Isra´ila

September 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuBe

Ƙungiyar Jihadil Islami,dake zirin Gaza, ta ɗauki alhakin harin da ya rutsa da wani sansanin sojojin Isra´ila.

A cewar kakakin ƙungiyar Hamas, Sami Abu Zuhri, wannan hari, da ya yi sanadiyar raunana sojojin Isra´ila kimanin 70, na matsayin shan fansa, ga hare-haren kan mai uwa da wabi, da bani yahudu ke kaiwa, kulluyaumin a zirin Gaza.

Tun shekara ta 2000, da saban rikicin ya ɓarke tsakanin Isra´ilawa da Palestinawa, wannan shine karo na farko, da Isra´ila ta samu sojoji masu yawa da su ka ji raunuka.

Hukumomin Isra´ila, sun bayyana maida martani a lokacin da ya dace, to saidai a cewar kakakin Hamas, cemma sun riga sun saba da irin wannan kalamomi, wanda ko mici ƙala zaratin, ba za su sa, su yi ƙasa a gwiwa ba a cikin gwaggwarmayar su, ta neman yanci.