1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jigilar jiragen ƙasa tsakanin Koriya ta arewa da Koriya ta kudu

May 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuLR

A karon farko cikin kusan shekaru 50, wasu jiragen ƙasa guda biyu sun fara safara a yankin nan da ya raba iyakar Koriya ta arewa da takwarar ta, ta kudu. An dauki tsawon lokaci ana ɗage safarar jiragen tun bayan da aka maida layin dogon da ya haɗe arewaci da kuma yammacin ƙasashen biyu shekaru hudu da suka wuce. Ministan hadin kan ƙasashen Lee Jae-Joung wanda ya jagoranci tawagar koriya ta kudu a cikin jirgin zuwa Koriya ta arewa ya baiyana maida safarar jiragen ƙasan a tsakanin ƙasashen biyu da cewa babban abin tarihi ne.