Jerin Gwanon Ista | Siyasa | DW | 09.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jerin Gwanon Ista

Dubban daruruwan mutane kan shiga zanga-zangar neman zaman lafiya a bukukuwan Ista a Jamus

Dubban Daruwan Mutane Suka Shiga Zanga-Zangar adawa Da Yakin Iraki Shekarar Da Ta Wuce

Dubban Daruwan Mutane Suka Shiga Zanga-Zangar adawa Da Yakin Iraki Shekarar Da Ta Wuce

Tun dai abin da ya kama daga farkon shekarun 1980 ne masu sha’awar zaman lafiya a nan kasar ta Jamus suka mayar da bukukuwan ista tamkar wata dama ta gudanar da zanga-zangarsu ta neman zaman lafiyar duniya. Sun kan shiga zanga-zangar adawa da kere-keren makaman kare dangi tare da gabatar da gargadi a game da irin masifar da wannan tserereniyar zata haifar ga makomar dan-Adam a duniya. A wancan zamanin dubban daruruwan mutane ne kan shiga wannan jerin gwano. Amma a ‚yan shekarun baya-bayan nan an samu koma bayan yawan masu sha’awar shiga a dama da su a zanga-zangar. Sai dai kuma a shekarar 1999 an samu karuwar masu zanga-zangar sakamakon farmakin da askarawan kungiyar NATO suka kai kan kasar Yugoslabiya da kuma shekarar bara domin adawa da yakin Iraki. A cikin watan fabarairun shekara ta 2003 an samu miliyoyin mutane da suka shiga zanga-zangar kyamar wannan mataki na soja akan kasar Iraki a sassa dabam-dabam na duniya. Amma dangane da jerin gwanon na ista wasu ‚yan dubbanin mutane ne suka shiga aka dama dasu saboda kafin wannan lokaci Amurka ta bayyana kawo karshen yakin a hukumance. To sai dai kuma duk da haka yakin Irakin ya taka muhimmiyar rawa a zanga-zangar da aka gudanar kuma haka lamarin yake dangane da wannan shekara ta la’akari da yadda al’amura suke dada rincabewa a kasar. A lokacin da yake bayani a game da mawuyacin halin da ake ciki Manfred Stenner kakakin gamayyar kungiyoyin fafutukar neman zaman lafiya a nan Jamus karawa yayi da cewar:

Wannan yakin ya haifar da mummunar kiyayya da kyamar kasashen yammaci a zukatan mutane a kasashen Larabawa da Afghanistan da Iraki ya kuma kara tsananta ayyukan tarzoma. Ta la’akari da haka kungiyoyin fafutukar neman zaman lafiya ke yin kiran bin manufofi na siyasa domin shawo kan rikice-rikice a cikin ruwan sanyi a maimakon matakai na soja dake kara rura wutar wadannan rikice-rikice. Abin takaici ma shi ne yadda gwamnati ke tsuke bakin aljifunta akan al’amuran da suka shafi kyautata jin dadin rayuwar jama’a a manufofinta na ketare, in kuwa da so samu ne da zata bukaci yin kari akan kasafin kudin soji na sama da Euro miliyan dubu 24 da aka tanadar.

Su dai kungiyoyin neman zaman lafiyar, kamar yadda Manfred Stenner ya nunar, ba su da wata takamaimiyar shawarar da zata taimaka a kawo karshen tashe-tashen hankulan dake dada kazancewa a kasar Iraki, amma akalla jerin gwanon na bukukuwan iska zai taimaka wajen wayar da kan jami’an siyasa cewar talakawan kasa na Allah Waddai da duk wani mataki na soja. Babu dai wasu tabbatattun alkaluma a game da yawan mahalarta zanga-zangar ta wannan shekara. A dai kwanakin baya-bayan nan an samu dubban daruruwan mutane dake halartar jerin gwano domin adawa da yakin Iraki da kuma matakan da gwamnati ke dauka na kayyade yawan abin da take kashewa domin kyautata jin dadin rayuwar jama’a a nan kasar.