1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jean Pierre Bemba ya bar Kinshasa zuwa Portugal

April 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuNu

Tsofan maitaimakin shugaban ƙasar Jamhuriya Demokradiyar Kongo,bugu da ƙari madugun yan tawaye, Jean Piere Bemba,ya bar birnin Kinshasa a sahiyar yau laraba, zuwa birnin Lisbon na ƙasar Portugal.

Tun ranar 22 ga watan Maris da ya wuce Jean Pierre Bemba ya samu mafakar siyasa a opishin jikadancin Afrikata Kudu, da ke birnin Kinshasa, bayan arangamar da aka gwabza, tsakanin dakarun sa da na gwamnati.

An bayyan cewar Bemba zai je ƙasar Porrtugal, domin binciken lahia , to saidai masu kula da al` ammura siyasa a Jamhuhiya Demokradiyar Kongo, na ɗaukar wannan bulaguro, a matsayin gudun hijira.

A wannan tafiya, ya samu rakiyar iyalan sa baki ɗaya.

Bayan mumunan kashin da dakarun madugun yan tawayen su ka sha, ranar 22 ga watan Maris gwamnatin shugaba Joseph Kabila, ta shiga neman sa ruwa jallo.