1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Westerwelle a taron Gamayyar Afirka a Kampala

July 22, 2010

Jamus ta sake jaddada neman goyon bayanta daga Afirka, a kokarinta na samun kujera a komitin Sulhu

https://p.dw.com/p/ORdz
Hoto: picture alliance / dpa

Ministan harkokin waje na tarayyar Jamus ya  nanata goyon bayan ƙasarsa wa baiwa  nahiyar Afirka zaunanniyyar kujera a komitin sulhun Majalisar Dunkin Duniya. Guido Westerwelle yayi wannan furuci ne a taron shugabannin ƙasashen Afirka a birnin Kampala.

Somalia Mogadischu US Militär 1992
Hoto: AP

A jawabinsa a wajen taron ƙungiyar gamayyar Afirka a birnin kamapalan ƙasar Uganda, Westerwelle ya bayyana bukatar wakilcin Afirka a komitin sulhu. Acewarsa Ƙungiyar Gamayyar Afrika tana da muhimman manufofin siyasa  na ƙasashen ketare, ya zamanto wajibi  ayi la'akari da  waɗannan kyawawan manufofi nan gaba, wanda ya dace a gani zahiri a komitin sulhun.

Ministan harkokin wajen na Jamus ya bada misalin irin rawa da ƙasashen Afirka ke takawa wajen yin ruwa da tsaki a warware rigingimu da wasu daga cikin ƙasashenta  ke fama da su.

A yanzu haka cewar Westerwelle, akwai tawagar Dakarun kiyaye zaman lafiya na gamayyar Afirka da ke girke a lardin Dafur dake yammacin Sudan da kuma ƙasar Somaliya masu fama da rigingimun 'yan tawaye.

" Muna sha'awar ganin cewar, an tallata kyawawan abubuwan da suke wannan nahiya, fiye da  yadda Duniya ke  mata kallon nahiya mai koma baya. Babu shakka Afirka nahiya ce mai tarin matsaloli da suka haɗar da rashin sanin makoma, har da ƙasashen da ba zamu iya cewa akwai doka ba. Amma a ɗaya ɓangaren kuma Afirka nahiya ce dake da ɗumbin dama, idan muka duba kamar Afirka ta kudu da ta jima tana taka rawa a fannonin cigaba. Jamus tana muradin kasancewa tare da wannan nahiya a kokarinta na inganata harkokin tattalin arziki da siyasarta"

To sai dai kazalika ministan harkokin wajen na jamus yana mika ƙoƙokin baransa ne dangane da nemarwa Jamus goyon baya daga waɗannan shugabannin na Afirka, a kokarinta na neman kujera a komitin sulhun Majalisar Ɗunkin Duniya. Tuni dai tarayyar Jamus ta gabatar da bukatarta na neman wannan kujera  a shekarun 2011 da 2012 masu gabatowa.

Karte Uganda mit der Hauptstadt Kampala Deutsch
Hoto: DW

Bugu da kari Westerwelle ya  jaddada bukatar kara bada muhimmanci wajen tallafawa ƙasar Somaliya da ke fama da rigingimu na 'yan Tawaye. Yace wannan ƙasa da ke kahon Afirka ta gaza samun ɗorarriyar gwamnati tun daga shekara ta 1990. Akasarin ƙasar na karkashin ƙungiyoyin tawaye ne na daban-daban da suka haɗar da na al-Shabaab.

" Ya zamanto wajibi mu yi aiki tare domin samar da zaman lafiya a Somaliya. Turai na goyon bayan Afirka , kuma zata yi aiki tare da wannan nahiya domin samar da ɗorarren  zaman lafiya a Somaliya"

A cikin kwanakin baya ne dai wasu masu tsattsauran ra'ayi na Somaliya suka tayar da boma bomai guda biyu a birinin Kampala ƙasar Uganda, harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 70. An danganta harin dai da sakawa Uganda da ƙungiyoyin suka yi, na tura Dakarunta kimanin 3,000  zuwa Somaliyan domin ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Zainab Mohammed Ahmad Tijani Lawal