Jawabin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a majalisar dokoki | Labarai | DW | 14.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a majalisar dokoki

A daidai lokacin da shugabannin KTT suka hallara a birnin Brussels don gudanar da taron kolin yini biyu, SGJ Angela Merkel ta yiwa majalisar dokoki jawabi akan manufofin Jamus bayan ta karbi shugabancin kungiyar EU. A farkon watan janeru kasar zata karbi shugabancin wata 6 na EU daga Finland. Merkel ta yi amfani da jawabin tana mai cewa fadada kungiyar zuwa gabashin Turai ta yi nasara.Ta yi kira ga kasashen kungiyar da su kara bawa juna hadin kai, don ta haka ne kawai za´a cimma manufar da aka sa gaba.