Jawabin Shugaban Palisɗinawa a taron Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa. | Labarai | DW | 08.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin Shugaban Palisɗinawa a taron Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa.

Yau shugaban Palisɗinawa zai bayyana masayinsa na ƙin shiga tattaunawa da Isra'ila.

default

President Mahmud tare da magoya bayansa.

Yau ake sa ran shugaban gwagwarmaya ƙwatar 'yancin Palisɗinawa, Mahamoud Abbas zai bayyana matsayinsa na kin ci-gaba da tattaunawa da ƙasar Isara'ila, a gaban taron ministocin harkokin waje na Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da ake gudanarwa a birnin Syrte na ƙasar Libiya. Abbas wanda ya ce a shirye ya ke ya ci gaba da yin tattaunawar ta kai tsaye da Isara'ila, idan har za ta dakatar da shirinta na gina matsugunan Yahudawa a yankunan Larabawa da ta mamaye a Gaɓar yamma da Ƙogin Jordan da kuma zirin gaza, na neman goyon bayan Ƙungiyar Ƙasahen Larabawan dangane da wannan taƙaddama da ke ɗaukar hankali ƙasashen duniya. Sannan kuma an shirya shugaba Abbas ɗin zai yi jawabi a gaban shugabannin ƙasashen na Larabawan a taron da za su buɗe a gobe Asabar idan allah ya kaimu.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas