Jawabin Shugaban Kasar Jamus Akan Girgizar Tsunami | Siyasa | DW | 31.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jawabin Shugaban Kasar Jamus Akan Girgizar Tsunami

Shugaban kasar jamus Horst Köhler yayi kira ga al'umar kasar da su ba da taimakon kudi domin bayin Allah da tsautsayi ya rutsa da su a kudancin Asiya

A lokacin da yake jawabi shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya kara ne da cewar a rayuwarsa ya shaidar da abubuwa masu tarin yawa na tausayi, musamman ma a shekarun baya-bayan nan, amma wannan tsautsayin da ya rutsa da yankunan kudanci da kuma kudu-maso-gabacin Asiya, wani bala’i ne daga Indallahi da bai taba ganin irin shigensa ba, kuma ya jefa shi cikin rudami da rashin sanin tabbas. A halin yanzu haka an tono gawawwakin mutane sama da dubu dari, a baya ga wasu dubban da ba a san makomarsu ba. Köhler sai ya kara da cewar:

Hatta a nan Jamus akwai mutane da dama da suka rasa ‚yan uwa da abokansu na arziki a wannan tsautsayi. Muna tausaya wa dukkan mutanen da har yau suke cikin rudami da rashin sanin tabbas a game da makomar ‚yan uwansu. Zukatanmu na tare da su da kuma ‚yan uwan nasu da kaddara ta rutsa da su."

Muhimmin abu a yanzun, kamar yadda shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya nunar, shi ne gabatar da taimakon gaggawa, kuma a saboda haka yake yaba wa gwamnati a fadar mulki ta Berlin, wacce tuni ta ware Euro miliyan 20 don taimako. Kazalika yayi marhabin da halin sanin ya kamata da Jamusawa suka nunar wajen ba da taimakon kudi gwargwadon ikonsu. Irin wannan taimako na gaggawa a cikin dan gajeren lokaci yana da muhimmanci matuka ainun, amma duk da haka wajibi ne a kuma sake tsara wani tsayayyen shirin taimako na dogon lokaci, abin da ya hada har da tsarin nan na gangami akan kari. A matsayinsa na tsofon darektan asusun ba da lamuni na duniya IMF Horst Köhler cewa yayi:

Wannan matakin kamata yayi ya hada da manufar sassauta basusussukan dake kan kasashen da lamarin ya shafa. A ganinsa wannan bala'in tamkar wata kafa ce da zata taimaka a sake bitar siyasar duniya domin ba ta wani sabon fasalin da ya dace. Wajibi ne a gane cewar dukkan ‚yan-Adam jirgi daya ne ke dauke dasu kuma a saboda haka ya kamata a rika bin wata siyasar gyara bai daya da kuma nagartattun manufofin raya makomar kasashe masu tasowa.