1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Shugaban Kasar Jamus A Knesset

February 3, 2005

A jawabin da ya gabatar ga wakilan majalisar dokokin Isra'ila, shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya ce kasar zata yi bakin kokarinta wajen murkushe 'yan adawa da Yahudawa da kyamar baki a siyasance

https://p.dw.com/p/BvdM
Hprst Köhler a Isra'ila
Hprst Köhler a Isra'ilaHoto: dpa

Shugaban na kasar Jamus wanda ke ziyarar Isra’ila domin bikin samun shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, ya gabatar da jawabinsa ne da harshen Jamusanci, wanda Yahudawa da dama ke kyamar saurarensa saboda tunasar da su da harshen ke yi a game da ta’asar kisan kiyashin da ‚yan Nazinhitler suka yi wa Yahudawa, wanda aka fi sani da Turanci Holocaust a takaice. An samu wasu daidaikun wakilan majalisar da suka kaurace wa zauren domin nuna kyamarsu ga jawabin Horst Köhler da harshen Jamusanci. To sai dai kuma shugaban na Jamus ya fara jawabin nasa ne da harshen hibru na Yahudawa, abin da ya haifar da rudami, sannan shi kuma kakakin majalisar dokokin Isra’ilar ya tuntsire da dariya. Amma wannan salon da shugaban kasar Jamus Horst Köhler yayi amfani da tashi ya taimaka wajen sararawar al’amura da tsaftace gurbataccen yanayin da ake ciki a zauren, kafin ya ci gaba da jawabinsa da harshen Jamusanci. Ba kuwa tare da wata rufa-rufa ba Horst Köhler ya ce har yau ba za a iya batu a game da wata huldar dangantaka dake tafiya salin-alin tsakanin Isra’ila da Jamus ba sakamakon ta’asar ta kisan kare dangi akan Yahudawa misalin shekaru 60 da suka wuce. Yayi bayani dalla-dalla a game da abubuwa na tausayin dake sosa zukatan dukkan masu kai ziyara sansanin gwale-gwalen nan na Auschwitz ko dandalin tunawa da wannan ta’asa da aka kebe a birnin Kudus. Köhler ya ce har abada ba za a manta da wannan dannyen aiki mafi muni da dan-Adam ya shaida a tarihinsa na wanzuwa ba. Babu dai wani mutumin da ya taba tunanin cewar za a samu wata kakkarfar hulda ta kawance tsakanin Jamus da Isra’ila a lokacin da suka kulla dangantakarsu ta diplomasiyya shekaru arba’in da suka wuce ba. A baya ga huldodi na siyasa da tattalin arziki da al’adu, kazalika akwai dangantaka ta kut-da-kut tsakanin al’umar kasashen guda biyu, duk kuwa da cewar an yi tsawon shekaru da dama a kasar ta Isra’ila ana samun wasu dake daukar cewa kowane Bajamushe dan-Nazi ne, mai alhakin kisan kai. Amma sannu a hankali al’amura sun canza suka dauki wani sabon fasali mai ma’ana, inda aka wayi gari an gusar da wannan akida ta gaba tsakanin sassan biyu. Jamus ce babbar abokiyar burmin cinikin Isra’ila a nahiyar Turai, wacce kuma ke magana da yawun Isra’ila a tsakanin KTT. Köhler ya ce tilas ne a kara karfafa wadannan huldodi na dangantaku saboda maslahar dukkan kasashen biyu. Shugaban kasar ta Jamus, kazalika ya fito fili yana mai tofin Allah tsine akan akidar adawa da Yahudawa da kyamar bakin dake dada zama ruwan dare a kasar, amma ya ce za a dauki nagartattun matakan da suka dace na wayar da kan mutane a siyasance.