1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Shugaba Mahmud Abbas ga Majalisar Dinkin Duniya.

September 25, 2010

Shugaban Falisdinawa ya yi kira ga Isra'ila da ta ci gaba da dakatar da gine-gine a yankunan da ta mamaye.

https://p.dw.com/p/PMlJ
Shugaba Mahmud Abbas.Hoto: AP

Shugaba Mahmud Abbas na Falasdinu ya yi suka ga dabi'ar Isra'ila na kokarin ci gaba da mamaye yankuna da kuma yin ruwa da tsaki a yankin. Shugaban na Falasdinu ya yi wannan furucin ne a cikin jawabin da ya yi wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya, wanda yanzu haka ke gudana a birnin New York na kasar Amirka. Shugaba Abbas ya ce ya rage wa Isra'ila ta zabi tsankanin rungumar cimma sulhu da Falasdinawa da ci gaba da gine - gine.

A halin da ake ciki kuma, sakatariyar kula da harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton za ta sake ganawa da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, a kokarin da take yi na shawo kansa ya yi watsi da furucin da ya yi na cewar zai fice daga tattaunawar zaman lafiya tare da Isra'ila - muddin dai ta ki sabunta wa'adin dakatar da gine - gine a yankunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan. Tuni dai Clinton da kuma Shugaba Abbas suka gana jiya Juma'a a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya, amma tattaunawar ba ta haifar da wani sakamakon a zo a gani ba. Isra'ila dai na shirin dage dakatar da gine - ginen da ta yi na wa'adin watanni goma a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Shugaban Amirka, Barak Obama da kuma shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, wadanda suka tattauna ta wayar tarho, sun bayyana bukatar Isra'ila ta tsawaita wa'adin dakatar da gine - ginen, kana ta ci gaba da tattaunawar neman zaman lafiyar, wadda sassan biyu suka jinginar tun kimanin watanni 18 kenan, kana suka sake fara ganawar kai tsaye a farko - farkon watan nan. A jiya Juma'a ce Isra'ila ta ce tana muradin kulla wata yarjejeniyar da za ta sami amincewar Amirka da Falasdinawa, amma shugaba Abbas ya yi watsi da sharuddan da ta gindaya.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas