1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jawabin shugaba Georges Bush na amurika

Shugaban kasar Amurika ya gabatar da jawabi inda ya bayyana manufofin gwamnatin Amurika a kan harakokin siyasar dunia da ta cikin gida

default

Kamar yadda ya saba lokaci zuwa lokaci, jiya ne shugaban kasar Amurika Georges Bush ya gabatar da jawabi inda ya bayyana manufofin gwamnatin Amurika a game da siyasar dunia, da ta cikin gida.

Bush ya tabo batutuwa daban daban, da su ka shafi tattalin arziki , demokradiya,da kuma halin da ake ciki, a yankin gabas ta tsakiya mussaman, a kasashen Iran, Iraki Palestinu da Isra´ila.

A dangane da abunda ya shafi tattalin arziki shugaban kasar Amurika , ya sannar cewa Gwamnati nza ta rage dogaro da kasasheh ketare ta fannin samar da man petur5.

Nan da shekara ta 2025, Amurika na hasashen ragewa, da kashi 75 bisa 100, na man Petur din da ta ke sayawa daga yankin gabas ta tsakiya.

A hannu z ata tanadi sabin hussa´o´I na samara da water lantarki ba tare da anfani da man Petur ba.

Kiiddigar da opioshinminisat mai kuzl adf harakokin man Patru ya gabatar na nuni da cewa kasashe 5 da su ka hada Tarraya Nigeria Saudi Arabia Venezuela Kanada da Mexique kew samar da kashi 67 bisa dari na daukacin man da Amurika ke anfani da shi.

Amurika a yan shekaru masu zuwa z ata anfanbi da wanna sabin hussa´o´i domin samar da makamashin ta ba tare da ta yio dogaro ba da kwetare, a gamed da haka Bush ya bayyana kari kashi 22 bisa 100 na kuddaden dav ake anfani da su dominsamar da makamashi.

Sannan yayi kira ga kurrarun masana na Amurika da su maida himma, wajen yada hikimar motoci masu anfani da ruwa a maimakon man petur.

Hakan zai rage mattuka gayya anfani da ma da kuma rege dumamar yanayi.

A game da abinda ya shafi Irak, kamar yada ya saba, Bush ya tabbatar da Amurika zata ci babbar galaba, a kan yan yakin sunkuru da ke ci gaba da tada zaune tsaye a wannan kasa.

Babu gudu babu ja da baya a game da yaki da yan ta´adar kasar Iraki, za mu ci gaba da bada babbar gudun muwa , har sai mun tabbatar da Iraki ta zama kasa mai cikkaken yanci, al´umomin ta na cikin kwanciyar hankali da lumana inji Bush.

Idan a cikin wannan mumunan yanayi mu ka hiddo sojojin mu daga Iraki, za mu bar al´ummar wannan kasa, ga jagorancin muttantani ire- iren su Usama Ben Laden ,da su Abu Mussab Zarkawi.

A game da kasar Iran kuwa, Georges Bush, ya yi suka da kaukausar halshe ga shugaban kasa Muhamud Ahmadi Nijad.

Kasar Iran ta shiga hannun wasu yan tsirarun mutane, masu tsatsaura ra´ayi ,da ke gana ukuba ga al´umma.

Kazalika, wannan mutane su ne ke rura wutar ta´adanci a kasashe kamar su Labanan da Palestinu.

Amurika za ta yi iya kokarin ta, don maido Iran bisa inganttatar turba ta Demokradiya inji shugaban Amurika.

A kan batun nasara da kungiyar Hamas ta samu, a zaben yan majalisun dokoki na Palestinu, Bush yayi kira ga shugabanin kungiyar da su gagauta ajje makaman kai hare haren ta´adanci, su kuma amince da kasar Isra´ila.

A daya hannun kuma, yayi kira ga kasashen Masar, Saudi Arabia, da Palestinu, da su ci gaba da tsarin shinfida mulkin demokradiya.

 • Kwanan wata 01.02.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1w
 • Kwanan wata 01.02.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1w