Jawabin shugaba Bush ga sojojin Amurka | Siyasa | DW | 25.08.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jawabin shugaba Bush ga sojojin Amurka

Duk da kalubalar da yake fuskanta, shugaba Bush bai dadara ba yana mai kare matsayin manufofinsa dangane da Iraki

Shugaba Bush na Amurka

Shugaba Bush na Amurka

A cikin jawabin nasa na farfaganda a gaban mutane kimanin dubu tara shugaba Bush ya kara da cewar sojojin Amurka zasu ci gaba da fafatawa a kasar ta Iraki har sai an cimma nasarar murkushe ta’addanci. Wannan jawabi na shugaba Bush dangane da kasar Iraki, shi ne karo na biyu a cikin ‚yan kwanakin da suka wuce domin mayar da martani akan karuwar yawan masu sukan lamirin manufofin shugaban na Amurka dangane da kasar Iraki. Shugaban ya ce ‚yanci da walwala hakki ne na kowa-da-kowa daga Indallahi. Sojojin da suka halarci dandalin jawabin tare da danginsu sun dokata da kalaman da suka ji daga bakin Shugaba Bush, musamman ma yaba musu da ya rika yi a game da gudummawar da suke bayarwa wajen yaki da ta’addanci. Wannan guda da tafi da shugaban Amurkan ya sha daga mahalarta dandalin jawabin nasa ba abin mamaki ba ne saboda dukkansu ‚yan amshin shatansa ne dake ko oho da ainifin matsalolin da ita kanta Amurka ke fama da su a kasar ta Iraki. Mutum na iya daukar lamarin tamkar abin ba a da dariya, in ba don mawuyacin halin da ake ciki ba. Domin kuwa sojojin Amurka 1900 suka yi asarar rayukansu banza da wufi dangane da manufofin shugaba Bush a Iraki, amma duk da haka shugaban na Amurka ya ki ya saduda ya hakikance da kura-kuran da ya caba na mamayar kasar Irakin. A baya ga gaskiyar cewa murna ta koma ciki dangane da hujjoji na kage da aka gabatar domin kai farmaki kann kasar da kuma doki da murnar da al’umarta suka yi game da shiga wani sabon babi na mulkin demokradiyya, masu sukan lamirin shugaba Bush na zarginsa da neman tilasta wa Irakawa su rungumi abin da ya kira wai baiwar ‚yanci daga Indallahi, alhali, a hakika tuni suka samu kansu cikin wani hali na bauta. Tun da dadewa wasu daga cikin jami’an siyasar Amurka suka ankara da haka, amma ba wanda ya saurari ta bakinsu a fadar mulki ta White House. A duk ko’ina ka waiwaya a kasar ta Amurka zaka samu dimbim masu adawa da wanzuwar sojan kasar a Iraki saboda wasu kwararan dalilai. Amma ga alamu janyewar Amurka daga wannan kasa zai zama tamkar tabarmar kunya ce da ake nade ta da hauka kuma martabar kasar zata zube a idanun duniya. A saboda haka ya zama tilas sojojin su ci gaba da wanzuwa a Iraki da kuma taimakawa akalla ko kasar ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. A takaice dai duk wanda ya nakalci lamarin baki daya zai ga cewar yakin an gabatar da shi ne akan wata hujja ta karya, kuma sanin kowa ne cewar karya ba ta fid da fure, a saboda haka aka fada cikin garari, wanda Amurka ce kadai ke da alhakin shawo kansa.