Jawabin saban shugaban Bankin Dunia | Labarai | DW | 31.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin saban shugaban Bankin Dunia

Saban shugaban Bankin Dunia Robert Zoellick, ya gabatar da jawabin farko, jim kaɗan bayan da shugaban Georges Bush na Amurika, ya bayyana shi a wannan matsayi.

Zoellick ya bayyana mahimman burinda ya ke ɗauke da shi a Banki Dunia, wanda da farko ya shafi maido da martar wannan banki, bayan abun kunyar da shughaba mai barin gado Paul Wolfowitz ya aikata.

Sannan ya bukaci dukan ƙasashe membobin bankin dunia, da jami´an da ke aiki a wannan banki, su ba shi haɗin kai don cimma burin da ya sa gaba.

Ya zuwa yanzu da dama daga ƙasashe masu faɗa a ji a wannan dunia, sun nuna goyan baya, ga Robert Zoellick , tare da yi masa kyaukyawar shaida.

Idan komitin zartaswa na bankin dunia, ya amince da naɗin, ranar 1 ga wata mai kamawa Zoellick zai gaji Wolfowitz.