1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janar David Petraeus ya yi jawabi a Brussels

Sadissou YahouzaJuly 1, 2010

Saban babban komandan NATO a Afganistan Janar David Petraeus ya bayyanawa shugaban NATO alƙiblar aikinsa a ƙasar.

https://p.dw.com/p/O8ZV
Jawabin Janar David Petraeus a cibiyar NATO dake birnin BrusselsHoto: AP

Saban babban kommandan na rundunar sojojin NATO a ƙasar Afganistan, Janar David Petraeus ya bayyana yiwuwar ƙarin hare haren ´yan taliban duk kuwa da matakan tsaro da NATO ta ɗauka.Janar Petraeus ya yi wannan jawabi, a yayin da yake ziyartar cibiyar NATO a birnin Brussels na ƙasar Beljiam.Ya ce ba za a samu wani cenji mai yawa ba, ga sallon yaƙin da magabacinsa, Janar Stanley McChrystal ya ƙaddamar.

Sai dai ya ce zai bada ƙarfi, wajen kare rayukan fararen hula, wanda ba su ci kasuwa ba, runfuna ke faɗa masu.

Janar Petraeus ya cigaba da cewar:

" Za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa , cikin fahintar juna, tsakanin sojojin Amirka da na ISAF, sannan a ɗaya hannun, tsakanin mu da dakarun Afganistan.Muddun muna buƙatar cimma nasara, dole sai mun haɗa kai."

Makon da ya gabata ne shugaban ƙasar Amirka Barack Obama ya sauke Janar Stanley McChristal daga shugabacin sojojin NATO bayan kalamomin ɓatancin da yayi wa fadar mulkin White House, sannan ya maye gurbinsa da Janar David Petraeus.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Ahmed Tijani Lawal