1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Papa Roma

December 26, 2005

Papa Roma Benedict na 16, ya yi wa dubban mabiya darikar katolika jawabi, a lokacin da ya jagoranci taron ibada na kirismeti a karo na farko, a dandalin St.Peters da ke daular Vatican.

https://p.dw.com/p/BvU6
Papa Roma, Benedict na 16.
Papa Roma, Benedict na 16.Hoto: AP

Daga barandar majami’ar St. Peters ta daular Vatican ne, a ran 19 ga watan Ifirilu na wannan shekarar, aka ba da sanarwar zaban Kardinal Joseph Ratzinger tamkar sabon Papa Roma, wanda zai maye gurbin marigayi Papa Roma John Paul na 2. Tun wannan lokacin ne kuma, sabon Papa Roman ya dau sunan Benedikt na 16. A jiya lahadi ne kuma, daga dai wannan barandar, Papa Roma Benedikt na 16, ya yi jawabinsa na gaisuwar kirismeti a karo na farko, zuwa ga dubban mabiya darikar katolika da suka taru a dandalin St. Peters, duk da ruwan saman da ake yi kamar da bakin kwarya. An dai kafa wani itacen kirismeti, mai tsawon mita 30, wanda aka kawo musamman daga Austriya.

Papa Roman ya yi kira ga mabiya darikarsa da su ba da imani ga Jesu al-Massihu da cewa:-

„Ya kamata, kowa daga jinsin bil’Adama na wannan zamanin ya mika hannu gare shi ba tare da wasu shakkku ba, ku ba shi damar shigowa gidajenku, da biranenku da jihohinku da ko wane lungu na wannan duniyar.“

Duk da ci gaban da aka samu a fannin kere-kere na kimiyya da fasaha a wannan zamanin, Papa Roman ya gargadi jama’a da kada su bari kyallin wadannan kayayyakin alatun su juya hankullansu daga addini. Ya kara da cewa:-

„Bil’Adama, a wannan zamanin na ci gaban kayayyakin masarufi, na huskantar barazanar zamowa bawan wadannan kayayykin. Ba ya amfani da hikima da basirar da Allah ya ba shi wajen daukaka ruhinsa zuwa ga ubangiji. Hakan kuwa na janyo dusashewar kwarjinin ransa da kuma bushewar zuciyarsa.“

Papa Roman dai ya kuma yi kira ga samar wa duniya baki daya, wani sabon yanayi na zaman lafiya da adalci. Sakon da ke kunshe cikin koyarwar addinin kirista na kaunar juna, zai iya bai wa bil’Adama kwazo da kuzari, wajen huskantar duk wani kalubalen da ke gabansa. Ta hakan ne kuma, inji shi, za a iya cim hadin kan bil’Adama, abin da a nasa bangaren zai iya taimakawa wajen warware matsaloli da dama da ake ta fama da su a halin yanzu a duniya, kamarsu ta’addanci da talauci, da yaduwar cututtuka da fataucin miyagun makamai da gurbacewar yanayi, wadanda duk suka zamo barazana ga makomar wannan duniya tamu. Har ila yau dai, Papa Roman ya kuma yi kira ga daukan matakan shawo kan rikice-rikcen da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin Darfur, da Latin Amirka, da Gabas Ta Tsakiya, da Iraqi, da Lebanon da makurdadar Korea, yankunan da yake gani kamar wato ya kamata a mai da hankali a kansu cikin gaggawa, kafin al’amura su kara tabarbarewa, har ababa su buwayi magancewa kuma.

A karshe dai Papa Roma, Benedikt na 16, ya mika gaisuwarsa ga al’umman duniya cikin harsuna 32, wato abin da ya zo kusan rabin harsunan da marigayi Papa Roma John Paul na 2 ke amfani da su a lokacin rayuwarsa.