1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Obama akan zagoyowar ranar 11/9.

September 10, 2010

Shugaban Amirka ya yi kira ga Amirkawa da su daina nuna kyama ga musulmai.

https://p.dw.com/p/P9Wo
Barack ObamaHoto: AP

Shugaban ƙasar Amirka Barack Obama ,ya gargaɗi Amirkawa kan ƙyamar addinin musulunci. Da yake jawabi a jajiberin cika shekaru tara da kai harin 11 ga watan Satumba, Obama ya kare Amirkawa musulmai, inda ya jinjina wa sojojin Amirka musulmai da ke fagen daga. Shugaba Barack Obama ya yi alƙawarin buɗe wani sabon babi a dangantakar Amirka da musulunci. A jawabin da ya yi wa manema labarai a fadar White House, Obama ya ce dukkannimu al'umma guda ce, wadda Allah ɗaya ya halitta, kuma muna rayuwa a ƙarƙashin ikonsa, sai dai kawai ko waɗanne su ƙira shi da suna daban, amma duk muna ƙasa ɗaya. Don haka ya ce maƙiyanmu sune ƙungiyar Alƙa'ida da ke son hallaka mu. Obama ya ce baya ga sojoji Amirkawa musulmai dake fagen daga a ƙasar Afganistan, akwai miliyoyin musulmai a ƙasar, 'ya'yansu na tafiya da namu makaranta guda, muna aiki tare a wuri guda, don haka idan muka nuna wa addininsu ƙyama, to me kenan muke faɗa musu? Shugaban na ƙasar Amirka ya kuma sake jaddada goyon bayansa ga gina cibiyar al'adun Islama da masallaci a kusa da inda aka kai harin 11 ga watan satumba a birnin New York.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas