Jawabin Mahamud Ahmadinedjad a taron Shangai | Labarai | DW | 15.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin Mahamud Ahmadinedjad a taron Shangai

Shugaban ƙasar Iran Mahmud Ahmadinedjad, ya gabatar da jawabi, a bikin buɗe taron, OCS, wato ƙungiyar mu´amila, da cuɗe ni in cuɗe ka, ta Shangai.

Ƙungiya ta ƙunshi ƙasashe 6, da su ka haɗa da Sin,Rasha,Kazakhstan,Kirgisthan,Tadjikistan da Ouzbebistan, sai kuma ƙasashen Mongolia, Iran,India da Pakistan da ke matsayin yan kallo.

A cikinj awabin da yayi, Ahmadi Nedjad, ya kira ga ƙasashe membonin ƙungiyar da su faɗaɗa ta, domin taka birki, ga ƙasashen da a halin yanzu, ke karyawa babu gaɓa, a dunia.

Ya ce wajibi ne, OCS ta rikiɗa, zuwa ƙungiya mai ƙarfi ta fannin tattalin arziki, siyasa da diplomatia, a yankin Asia da ma faɗin dunia.

Cimma wannan mataki, zai sa a samu sa´ida, ga shiga sharo ba shanu, da manyan kasahen ke yi, cikin harakokin da ba su shafe su ba, a ƙasashe daban-daban.

Gobe ne idan Allah ya kai mu, a karro na farko, Mahamud Ahmadinedjad, zai gana da takwaran sa na China, Hu Jin Tao.

A na kauttata zaton, sun tanttata batun rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran, wanda a halin yanzu, a ke ci gaba da kai ruwa rana kan sa, a fagen diplomatia na dunia.