1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

JAWABIN GADHAFI NA LIBYA GA YAN JARIDU

December 23, 2003
https://p.dw.com/p/Bvmy
Mahukuntan kasar Libya sun shaidar da cewa babu wani abu da suke dashi na boyewa dangane da makaman nukiliya,musanmamma bisa laakari da cewa yanzu kasar ta sanar da cewa ta dawo daga rakiyar da take dashi a baya na kera makaman nukiliyar. Haka kuma kasar ta Libya ta kara da cewa wannan mataki data dauka na watsi da aniyar tata ta makaman nukiliyar,matakine daya kamata,kasashe irin su Koriya ta arewa da iran da Syria suyi koyi dashi don samun tabbataccen wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a doron kasa baki daya. Wadan nan nan dai kalamai sun fito ne daga bakin shugaba Mohd Gahdafi,a laasariyar jiya litinin lokacin da yake zantawa da yan jaridu,a wani kauye wajen birnin tripoli. Shugaba Gadhafi yaci gaba da cewa,irin wannan daukar mataki na kassar tasa ya zamo wajibi,ga sauran kasashen daya ambata a baya,bisa dalilin tserar da darajar kasar da kuma kaucewa wulakancin da mutanen kasar zasu fuskanta,sakamakon irin daukar wannan mataki. Bugu da kari shugaba Gadhafi ya kumaci gaba da cewa, daukar mataki irin na kasar sa ga wadannan kasashe na sama shi zai taimaka wajen takura kasar Israela,ta fito fili tayiwa mutanen duniya bayani dangane da zargin da ake mata na mallakar wadan nan makamai na nukiliya. Har ila yau shugaba Gadhafi ya kara da cewa kasar sa bata da makami na nukiliya ko kuma mai sanya guba,sai dai a baya ta fara tattara wasu sanadarai da, za,ayi amfani dasu wajen kera makami na nukiliya. A yanzu haka kuma bisa laakari da irin halin da ake ciki a duniya yaga cewa yafi dacewa ya bayar da hadin kai ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya,don halaka ire iren wadan nan sanadarai da kuma wasu kananan makamai masu hatsari da kasar take dasu. Da kuwa yan jaridu n suka tambayi Gadhafi ko shin takunkumin da kasar Amurka ta lakabasa,nada nasaba da wannan mataki daya dauka,saiya kada baki yace,shi dai ya tabbatar da cewa matakin da kasar sa ta dauka mataki ne daya dace a dai dai wannan lokaci,kuma ya tabbatar da cewa zai kara dankon zumunci da fuskantar juna a tsakanin kasar sa da kuma sauran kasashen duniya. Kuma yin hakan a cewar sa zai taimakawa kasar samun taimako na ilimin ci gaban kimiyya da fusaha daga wasu kasashe na duniya da sukaci gaba a fannonin biyu. Kasar dai ta Libyaa baya tasha fama da takunkumi da kasar Amurka ta saka mata,sakamakon zarginta da tayi na cewa tana daurewa yan taadda gindi a shekara ta 1986,da kuma wanda ta sa mata a shekarar 1982 na hana shigo da danyan man fetur din kasar. Daga wadan nan kuma sai wanda MDD ta saka mata a shekarar 1988, na zargin ta datayi na cewa tana da hannu cikin hatsarin jirgin nan na Lockerbie daya kashe mutanen yamma kusan 270. A yanzu haka dai tuni MDD ta dagewa kasar takunkumin data saka mata,sakamakon yarda da mahukuntan kasar sukayi na biyan iyalan wadanda hatsarin ya rutsa dasu diyya, Haka kuma ana sa ran cewa nan bada dadewaba itama kasar Amurkan zata dagewa kasar ta Libya takunkumin data saka mata.