Jawabin Brahimi wa Komitin sulhu a jiya talata. | Siyasa | DW | 28.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jawabin Brahimi wa Komitin sulhu a jiya talata.

Jakadan MDD a Iraki,Lakhdar Brahimi ya gatarwa Komitin sulhun Majalisar,bukatar nada wakilan gwamnatin riko a Iraki,a watan mayu mai tsayawa.

Lakdar Brahimi yana gabatarwa komitin sulhu shiri akan gwamnatin riko a iraki.

Lakdar Brahimi yana gabatarwa komitin sulhu shiri akan gwamnatin riko a iraki.

Jakadan MDD Lakdar Brahimi ya fadawa taron komitin sulhu na majalisar a jiya cewa,ya zamanto wajibi a zabi wadanda zasu zasu kasance a gwamnatin riko na kasar Irakin a karshen watan Mayu mai tsayawa,wanda hakan ne zai basu daman kasancewa kann wannan matsayi na wata guda,kafin su daidaita kann sabuwar yarjejeniya da dakarun taron dangi da Amurka kewa jagoranci a karshen watan yuni,wadanda zasu cigaba da kula da harkokin tsaro a Irakin.

Jakadan yace akwai matsaloli masu yawan gaske dake tattare da wannan shiri ,amma zaa iya gudanar dashi ,duk da karuwan rikice rikice daya haddasa asaran rayukan daruruwan yan Iraki,da wasu dakarun taron dangin musamman a yan makonni da suka gabata.

A daidai lokacin da Brahimi ke wannan gabatarwa wa wakilan komitin suhun majalisar dunkin duniya da yammacin jiya,sojojin taron dangin sun kaddamar da wani hari a garin Falluja,abunda ke dada tabbatar dacewa da sauran rina a kaba a dangane da gano bakin zaren warware rikicin na wannan yanki.Wannan harin na jiya dai ya auku ne bayan dakarun Amurkan sun kashe wasu mutane 64 a kusa da garin Najaf dake kudanci,wadanda kuma suka kira yan bindiga dadi.

Brahimi yace babu abunda ya rage face gaggauta bawa yan Irakin mulkin kai,inda ya danganata wadannan tashe tashen hankula da Irakin ke fuskanta da rashin zaunanniyar gwamnatin mulkin kai.

Tsarin da jakadan MDD ya gabatar da i ya kunshi cewa,Gwamnatin rikon na Iraki zata tafi da dukkan harkokin gudanarwa a Irakin da zarar ta karbi akala ranar 30 ga watan yuni,kana zata jagoranci kasar zuwa zaben kasa baki daya a karshen watan janairun shekara ta 2005,idan mai duka ya kaimu.Sai dai yayi gargadin cewa zaa fuskanci matsaloli iri iri a kowane mataki,kafin ajega cimma tudun dafawa kann daidaita Iraki.

Brahimi ya fadawa komitin sulhun cewa akwai bukatar hada karfi da karfe wajen tabbatar da nasaran kafa gwamnatin kai a Iraki.

To sai dai wakilan komitin sulhun sunyi maraba da wannan gabatarwa na Brahimi wajen kafa gwamnatin riko,ayayinda a hannu guda suka gabatar da tambayoyi masu yawan gaske ,wadanda kuma basu samu amsarsu ba saboda har yanzu da sauran rina a kaba dangane da nadin wakilan gwamnatin rikon.

Jakadan Amurka John Negroponte yace Brahimi yayi kyakkyawan gabatarwa,amma dole a dauki matakin tabbatar da nasaran hakan a zahiri ba a rubuce kadai ba.Shi kuwa jakadan Britania Emyr Jones Parry ,yayi fatan zaa samu sakamakon tambayoyin da suka gabatar nan da yan watanni masu gabatowa,ayayinda mataimakin Jakadan Rasha Gennady Gatilov,yace dukkan gabatarwan na bisa tsari,to sai dai yayi nuni dacewa ko shi Brahimi bashi da tabbacin tabbatar da hakan a zahiri.Wata babbar matsala inji shi itace,yadda zaa zabi Prime minista,shugaban kasa da kuma mataimakan shugaban kasar guda biyu,wadanda Brahimin yace zasu kunshi gwamnati.

To sai dai Jakadan majalisar dunkin duniya yace ,yan kasar ta Irakitare da hadin gwiwan mdd da kasashen dake da sojojinsu a kasar ,nada rawa da zasu taka na zaban wakilai masu gaskiya,wadanda kuma zasu yi adalci cikin harkokin kasa ba tare da nuna son kai ko kuma cimma burin siyasa ba.

Brahimi yace dole ne acimma daidaito a dangane da matsayin gwamnatin rikon kwarya da zaa nada a hannu guda,da sojojin taron dangin da zasu cigaba da kasancewa a Irakin bayan 30 ga watan yuni,kana da Amurka dake jagoranci a halin yanzu.Kimanin dakaru dubu 150,zasu cigaba da kasancewa a Irakin,wanda zai bawa sabuwar gwamnatin,majalisar dunkin duniya da komitin sulhu tattauna yadda zaa tafi da alamuran wannan kasa.To sai dai Negroponte, wanda shugaba George W Bush ya nada a matsayin jakadan Amurka a Iraki bayan 30 ga watan Yuni,yayi nnu ni dacewa batun tsaro zai cigaba da kasancewa a karkashin sojojin taron dangin,amma ba gwamnatin rikin ba.

Zainab AM Abubakar.