Jawabin Angeller Merkel a Majalisar dokokin Bundestag | Labarai | DW | 30.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin Angeller Merkel a Majalisar dokokin Bundestag

Yau ne sabuwar shugabar gwamnati Jamus, Angeller Merkel ta yi jawabin farko gaban majalisar dokokin Bundestag tun bayan zaben ta a wannan mukami a satin da ya wuce.

Merkel ta tabo batutuwa daban daban, da su ka shafi siyasar dunia da ta cikin gida, da kumam passalin gwamnatin da ta ke jagoranta, na farfado da tattalin arzikin Jamus, da halin yanzu ke fuskantar tsaka mai wuya.

A game da batun yaki da ta´adanci ta sannar cewa ,Jamsu za ta aiki, kafada da kafada da sauran kashen dunia, domin fuskantar wannan barazana da ta zama ruwan dare.

Ta kuma fadi da babbar murya cewa , gwamatin Jamus zata har makura iya kukarin ta na ganin yan yaki sukurun Iraki, sun sako bajamusar da su ka yi garkuwa da ita.

Angelller Merkel, ta gargadi kasar Iran da ta gaggauta komawa tebrin shawara, da kasashen dunia, domin warware matsalar makaman ta, na Nuklea cikin ruwan sanhi.

Sannan ta bayya matukar murna, da gamsuwa, da hakin kan da a ka samu, tsakanin manyan jam´iyun Jamus, domin girka gwamnatin hadin gwiwa.