Jawabin Angela Merkel a Majalisar Turai | Siyasa | DW | 17.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jawabin Angela Merkel a Majalisar Turai

Tun bayan hawan kujerar shugaban KTT,wannan shine karon farko da shugabar ta Jamus tayi jawabi a gaban majalisar

Angela Merkel A gaban Majalisar Turai

Angela Merkel A gaban Majalisar Turai

A yau ne shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel tayi jawabinta na farko a gaban yan majalisar kungiyar tarayyar Turai a Strasbourg din kasar faransa,inda ta bayyana tsoron tarihin gazawar kungiyar a baya na cimma wani tudun dafawa dangane da kundun tsarin mulkinta.

Shugabar gwamnatin na jamus wadda kasarta ce a halin yanzu ke rike da kujerar shugabancin KTT tun daga ranar daya ga watan janairin da muke ciki,ta fara jawabin nata ne dayin nadama adangane da cimma matyayi guda a wannan kungiyar…..

“Duk kan iya rayuwata nayishine a anan turai,sai dai a wannan kungiya ta tarrayar turai zance har yanzu ni jaririya ce acikinta.Bayan hadewar jamus,na samu cudanya da mutane daban daban daga sauran kasashen turai,kuma zan iya cewa nasan harkokin kungiyar tarayyar turai har zuwa shekaru na 35.Na kan hangi lamura na kungiyar daga nesa, amma tun daga sheakra ta 1990 new na fara lura da harkokinta na cikin gida.

Shugabar gwamnatin na jamus ta fawa yan majalisar cewa akwai bukatar dukkannin kasashen wannan kungiya suyi aiki tare domin samar mata makoma ta gari.Tace wannan kuwa zai taallaka ne akan samar mata kundun tsarin mulki data jima tana fuskantar matsaloli dangane da ita.

Merkel ta bayyana rashin jindadinta dangane da sakamakon kuriun raba gardama da akayi a kasashen Faransa da netherlands.Inda ta jaddada cewa a watanni shida da Jamus zata rike kujerar shugabancin wannan kungiya ta tarayyar turai,zatayi kokarin cimma burimmu da ta sanya gaba dangane tabbatar da wannan kundi na tsarin mulkinta.

“Adan gane da hakane muke bukatar kwawwararru daga wannan kungiya da biranenta ,lokacin tunan baya ya shige,muna da lokaci daga yanzu zuwa watan yuni na samarwa wannan kungiya makomar darta dace da iata.Fatan na ayau shine, ya zamanto lokacin da Jamus zata mika kujerar shugabancin wannan kungiya an samu cigaba adangane da wannan kundundu na tasrin mulki”

Shi kuwa a nashi bangaren shugaban majalisar dokokin turai Hans-Gert Pöttering cewa yayi a shirye suke su bada hadin kai wa shugabar gwamnatin Jamus domin cimma manufofinta.”

Da wannan jawabi nata a gaban yan majalisar tarayyar turan,Angela Merkel ta fayyace musu manufofin ta musamman ma adangane da yadda jamus zata tafiyar da jagorancin wannan kungiya na tsawon watanni shida.

Bugu da kari Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kuma tabo manyan batutuwan nan biyu da suka hadar da taimakon rayakasashe da da kuma samarda ayyukanyi,bisa laakari da matsaloli da kasuwanni kwadago ke fama dasu a yanzu haka,a ilahirin turai baki daya.

Kazalika Angela Merkel ta jaddada manufofin kungiyar a karkashin jagorancin jamus,na duba halin ada ake ciki a yankunan da ake fama da rigingimu musamman yankin gabas ta tsakiya da Afganistan da yankin Balkan,inda take saran gabatar da wadannan batutuwa gaban taron kungiyar ta Eu dazai gudana a watan Maris da kuma taron kungiyar kasashe masu cigaban masaantu na G8.

Yanzu haka Dai Angela Merkel itace shugaba dake da rinjaye bayan Tony Blair da Jacques Chirac dake barin kujerun mulki cikin wannan sheakara a nahiyar turai,kuma zaben kasa baki daya dazai gudana nada matukar tasiri a dangane da makomar kungiyar ta Eu.