Jawabin Amr Musa a taron UNESCO | Labarai | DW | 31.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin Amr Musa a taron UNESCO

Sakatare Janar na ƙungiyar ƙasashen larabawa, Amr Musa, ya bayana aniyar tuntuɓar komitin sulhu na MDD, a game da abinda ya kira , ɓarkewar wani sanban babe na rikici, tsakanin manufofin ƙasashen yammacin dunia da addinin Islama.

Amr Musa, ya yi wannan huruci, albarkarin taron hukumar MDD, mai kulla da tarbiya, kimiya da al´adu, wato Unesco, da ke ci gaba da wakana, a birnin Paris na ƙasar France.

A jawabin nasa, Amr Musa, ya bayyana babbar barazanar da zaman cuɗe ni –in cuɗe ka, ke fuskanta, tsakanin kasashen musulmi da yammacin dunia, a dalili da abinda ƙasashen su ka kira, yaƙi da ta´danci.

Ya kuma kira ga ƙasashen, su daina yi wa musulunci mumunar fahinta, ta hanyar ɗaukar sa adinin tada hankali, da tsautsauran ra´ayi.